Hussein Mohammed Barre, kwamishin gunduma na garin Barawe a unguwar Lower Shabelle ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin din nan cewa, mutumin 'dan asalin kasar Amurka, jami'an tsaro dake yawon sintiri ne suka kame shi lokacin da yake kokarin tserewa daga kungiyar ta al-Shabaab bayan da aka kashe wassu abokan shi a wani fada tsakanin su.
Mr Barre ya yi bayanin cewa, wannan 'dan kasan wajen ya shaida masu cewa, shi 'dan asalin kasar Amurka ne, yana kuma jin turanci, sannan bakin fata ne tsakanin shekaru 30-40, amma ba'a sanar da sunan shi ga manema labarai ba.
Bayan tambayoyin da aka yi masa, ya bayyana cewa, yana kokarin tserewa ne daga 'yan kungiyar bayan da ya ga sun kashe abokan shi, don haka sai yana zaune cikin fargaba a kullum.
Ya ce, mutumin da ya fice daga kungiyar ta al-Qaida, ana da tabbacin cewa, ya koma kungiyar IS ne, mai sansani a kasar Syria kuma hakan ya kawo babbar takaddama tsakanin kungiyar ta al-Qaida mai alaka da al-Shabaab.(Fatimah)