in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 20 suka hallaka, 120 suka jikkata a wata arangama a Somaliya.
2015-12-09 11:05:01 cri

Rahotanni daga birnin Mogadishu na kasar Somaliya ya tabbatar da cewar a kalla mutane 20 ne suka hallaka sannan wadansu 120 suka jikkata a wata arangama tsakanin jami'an tsaro dake adawa da junansu a garin Galkayo dake tsakiyar kasar, in ji ofishin MDD.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalissar a sanarwar da ta fitar ta ce, mutane fiye da dubu 90 suka rasa muhallansu a cikin makonni biyu da aka dauka ana tashin hankali tsakanin jami'an tsaro a gundumomin mulki na Galmudug da Puntland.

Wannan tashin hankali ya kara rikita yanayin jin kai da a baya ake ta kokarin shawo kan shi a garin na Galkayo da kewayen shi, musamman mutanen da suka rasa muhallansu, da suke zama a sansanonin da da ma can suka fuskanci ruwan sama mai karfin gaske da yake kawo fargaba.

Sai dai kuma an samu dan sassauci a garin na Galkayo bayan rattaba hannu na dakatar da bude wuta. Rahotanni ya tabbatar da cewa, jami'ai masu dauke da makamai daga dukkan bangarorin biyu sun fara janyewa daga fagen daga, inji MDD.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China