in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 2 sun rasu sakamakon fashewar boma-bomai a Somaliya
2016-01-03 14:12:09 cri
Rundunar 'yan sandan dake babban birnin kasar Somaliya, Mogadishu ta gaskata cewa, an kai harin bom iri na kunar bakin wake a wani hotel a ran 2 ga wata, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla guda biyu, yayin da wasu suka jikkata.

Haka kuma 'yan sanda sun bayyana cewa, hotel din da dakarun suka farma yana kusa da fadar shugaban kasa ta Somaliya, a halin yanzu kuma, 'yan sanda sun riga sun isa wurin domin gudanar da bincike.

Haka kuma, wasu mazauna wurin sun bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, bayan da suka ji fashewar boma-bomai, sun gudu daga wurin, tare da nuna damuwa kan sake abkuwar wani harin a wurin

Bugu da kari, wasu ganau sun bayyana cewa, fashewar boma-bomai sun lalata motoci da dama.

Haka kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, kungiyar Al-Shabab ta Somaliya ta taba kai hare-hare a wannan hotel. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China