in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hare-hare a babban birnin kasar Somaliya
2015-12-20 14:01:32 cri

Rundunar 'yan sandan kasar Somaliya ta gaskata cewa, an kai hare-haren bindigogi da boma-bomai a cibiyar babban birnin kasar, Mogadishu a ran 19 ga wata, wadanda suka haddasa rasuwar mutane guda biyu, yayin da goma suka jikkata.

Wani jami'in 'yan sandan ya bayyana cewa, an kai hare-hare a wata hanyar mota dake birnin Mogadishu, kuma galibin wadanda suka rasu ko jikkata fararen hula ne, kuma wani shugaban 'yan sandan wurin ya ji rauni.

Wasu ganau sun bayyana cewa, maharban sun fara bude wuta kan motar jami'an gwamnatin kasar, sa'an nan, an yi musayar wuta a tsakanin maharan da masu kiyaye tsaro, haka kuma, wata mota dake dauke da boma-bomai ta fashe bayan da 'yan sanda suka isa wurin musayar wuta.

Sojoji da masu aikin ceto sun isa wurin a lokacin barkewar hare-haren, tare da killace wurin. Ya zuwa yanzu, babu wanda ko wata kungiyar da ta dauki alhakin kai hare-haren, amma, 'yan sanda na ganin cewa, mai yiyuwa ne kungiyar al-Shabaab ta kai wadannan hare-hare. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China