in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Somaliya sun harbe 'yan kungiyar al-Shabaab guda 13
2016-01-15 10:47:30 cri
Sojojin gwamnatin kasar Somaliya sun yi nasarar harbe 'yan kungiyar al-Shabaab guda 13 a yayin wata musayar wuta da bangarorin biyu suka yi a yankin tsakiyar kasar.

Haka kuma, wani jami'in wurin ya tabbatar da cewa, sojojin gwamnatin sun yi nasarar a kan dakarun kungiyar al-Shabaab ne bisa taimakon rundunar sojan kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU da ke kasar, inda aka kashe a kalla 'yan kungiyar al-Shabaab guda 9 a musayar wutar da suka yi.

Bugu da kari, sojojin gwamnatin sun kashe 'yan kungiyar ta al-Shabaab guda 4 a yayin wata musayar wuta a jihar Hiran dake yankin tsakiyar kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China