in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barack Obama ya sanar da matakan kayyade mallakar bindigogi a Amurka
2016-01-06 10:49:07 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya sanar da jerin matakan da gwamnatin sa za ta dauka, na kayyade mallakar bindigogi a kasar sa a jiya Talata 5 ga wata, a wani mataki na dakile hallaka al'ummar kasar ta hanyar amfani da bindigogi.

Mista Obama wanda yake tare da iyalan wadanda suka rasa iyalan su sakamakon wannan matsala, ya gudanar da taron manema labaru a fadar White House, inda da kakkausar murya ya bayyana barazanar da wannan matsala ke haifar, tare da sanar da cewa, tilas ne duk wanda zai sayar da bindiga ya sami izni daga gwamnati, tare da yiwa wanda zai sayi bindiga cikakken bincike, kuma sabawa hakan zai sanya mutum fuskantar shari'a.

A cewar Obama, gwamnatin sa za ta yi hayar karin mutane don gudanar da aikin bincike kan wadanda za su sayi bindiga, da kuma kara yin hayar masu bincike 200 don tabbatar da aiwatar da wannan doka yadda ya kamata. Baya ga haka, gwamnatin za ta zuba kudi dala miliyan 500, don ba da kulawa ga wadanda suke kamu wa da cututtukan tabin hankali.

Ban da haka, Mista Obama ya ce Amurka ita ce kadai kasar dake shan fama da laifuffuka dake da nasaba da bindiga, inda a kalla mutane dubu 30 suke rasa rayukansu a ko wace shekara saboda wannan matsala.

Hakan a cewar sa ya wajabta daukar matakan dakile wannan matsala. Bugu da kari shugaba Obama, ya kara yin suka ga majalissar dokokin kasar, bisa gaza daukar wani mataki na warware wannan matsala, tare kuma da kalubalantar majalisar da ta zartas da dokar kayyade mallakar bindiga, don kawo karshen laifufukan dake da nasaba da bindiga. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China