in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An halaka shugabannin IS guda 10 a wani hari ta sama da sojojin Amurka suka kaddamar
2015-12-30 11:17:34 cri
Ma'aikatar tsaron Amurka ta tabbatar a jiya cewa, a watan nan da muke ciki, an halaka shugabannin kungiyar IS guda 10, a hare-hare ta sama da kawancen kasa da kasa da Amurka ke jagoranta ya kaddamar kan sansanonin kungiyar. A cikinsu kuwa, akwai wani da ake zargi da hannu a harin da aka kai birnin Paris na kasar Faransa a watan da ya gabata.

Haka kuma, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Amurka Steve Warren ya ce, dakarun kawancen kasa da kasa sun yi nasarar halaka jagoran kungiyar IS mai suna Abdelhamid Abaaoud dake boye a kasar Syria, a wani hari ta sama da dakarun kawancen suka kai a ranar 24 ga wata.

Bayanai na nuna cewa, Abdelhamid yana da alaka kai tsaye da Sharafe Mu Adan mutumin da ake ganin shi ne ya jagoranci harin da aka kai a birnin Paris na kasar Faransa cikin watan da ya gabata. Warren ya kuma kara da cewa, Sharafe Mu Adan yana shirya wasu hare-haren da kungiyar za ta kai a wasu kasashen yammacin duniya.

Bugu da kari, Warren ya ce, dakarun kawancen kasa da kasa za su ci gaba da nema da kuma halaka dukkanin shugabannin kungiyar IS dake da niyyar kaiwa Amurka da kawayenta hare-hare. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China