in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Amurka da Cuba sun tattauna kan inganta hadin gwiwarsu
2015-09-30 10:45:34 cri
Shugaban kasar Amurka Barack Obama da takwaransa na kasar Cuba Raúl Castro sun yi shawarwari a cibiyar MDD dake birnin New York a jiya Talata 29 ga wata, inda suka tattauna kan ci gaban da aka samu kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tare da yadda za a kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu.

A ranar litinin ne, shugabannin kasashen Amurka da Cuba bi da bi suka yi jawabi a gun muhawarar babban taron MDD. A jawabin sa Shugaba Obama ya nuna imanin da cewa, majalisar dokokin kasar Amurka za ta soke manufar hana yin jigilar kaya zuwa ga kasar Cuba. Shi kuma a nashi jawabin Shugaban na Cuba Raul Castro kira ya yi ga kasar Amurka da ta soke takunkumin da ta sanya ma kasarsa a fannonin tattalin aziki, cinikayya da hada-hadar kudi. Haka kuma ya bukaci kasar Amurka da ta mayar da yankin Guantanamo da samar da diyya ga jama'ar kasar Cuba wadanda suka samu hasarori da dama a shekaru fiye da 10 da suka wuce. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China