Taron wanda ya gudana a nan birnin Beijing, ya samu halartar shahararrun masana da kwararru na Sin da Amurka kimanin 20. Yayin zantawar tasu da manema labarau, sun bayyana cewa, kasashen Sin da Amurka suna da ra'ayi irin guda game da muhimman batutuwa, sabo da haka, inganta tuntubawa da kara hadin gwiwa ya zama babban jigo na raya dangantakar bangarorin biyu.
Shugaban kwamitin nazarin dangantakar da ke tsakanin Amurka da Sin Stephen A. Orlins ya ce, batun yaki da ta'addanci da na sauyin yanayi, da na kiyaye muhalli, da na samun bunkasuwar tattalin arziki, sun kasance batutuwan da kasashen biyu suke dora muhimmanci sosai a kansu. Don haka a cewarsa ya zama dole bangarorin biyu su fuskanci wadannan batutuwa tare. Ya ce su ma jama'ar kasashen biyu suna maida hankali kan wasu batutuwa kusan iri guda, kamar batun samun albashi, da ilmi, da inshorar lafiya.
A nasa bangare, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai lura da yankin gabashin Asiya da tekun Fasific Evans J.R. Revere, ya bayyana farin cikin sa game da dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu. Ya ce, abun da ya fi muhimmanci shi ne, yadda bangarorin biyu ke samun daidaito, da kawar da sabanin da ke tsakaninsu, matakin da ke bukatar sanya idon basira daga bangaren shugabannin kasashen biyu, kana ya ce ya kamata a inganta mu'amala tsakanin masana da kwararru.(Bako)