Jakadan Cui ya ce, kutsa kai cikin ruwan kasar Sin da jiragen ruwan yaki na Amurka suka yi ya zama babbar barazana, kuma kasar Sin da jama'ar kasar dake fatan samar da zaman lafiya a wannan yanki sun dora muhimmanci sosai game da lamarin.
Ya kara da cewa, matsayin da Amurka ke tsayawa a kai game da batun tekun Nanhai tamkar almara ce. A bangare guda ma, ta bukaci sauran bangarorin da kada a rura wuta ta hanyar yin shisshigin soji a yanki, sannan a dayan bangare, ta tura jiragen ruwan yaki zuwa yankin.
Jakadan Cui ya sake nanata cewa, kasar Sin na da ikon mulkin kai a tekun kudancin ta tun asali. Har ila yau in ji Mista Cui,Kasar Sin za ta dauki kwararran matakai don tabbatar da cin gashin kanta da cikakken ikonta, don samar da zaman lafiya da karko a yankin.(Bako)