Guo Shengkun ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a kasar Amurka a watan Satumba cikin nasara, shugabannin kasashen biyu sun cimma daidaito kan batun tabbatar da tsaron internet, kuma sun tsaida kudurin kafa tsarin tattaunawa kan yaki da laifuffukan da aka aikata a kan internet.
Lynch da Johnson sun bayyana cewa, a matsayin manyan kasashen tattalin arziki a duniya, Amurka da Sin suna da moriya iri daya a fannin tsaron internet. Amurka tana son daukar matakan da shugabannin kasashen biyu suka cimma cikin sahihanci.
A gun taron tattaunawar, bangarorin biyu sun cimma ka'idojin yaki da laifuffukan da aka aikata a internet da sauran batutuwan da abin ya shafa, sun tsaida kudurin kafa tsarin layin musamman na tarho, da cimma daidaito kan warware matsalolin dake shafar tsaron internet, hadin gwiwar yaki da ta'addanci a internet, horar da kwararru a wannan fanni da dai sauransu. (Zainab)