Shugabannin biyu sun gana ne a jiya Litinin, kuma wannan ne karo na farko da Obama da Netanyahu suka hadu bayan kusan sama da shekara guda. Rahotanni sun bayyana cewa makasudin ganawar tasu shi ne kyautata dangantakar dake tsakanin Amurka da Isra'ila.
A baya dai cikin watan Maris da ya gabata, Netanyahu ya gabatar da jawabi a majalissar dokokin kasar Amurka, inda ya nuna adawar sa game da manufar kasar don gane da shigar ta shawarwari tare da Iran kan batun nukiliyar kasar ta Iran.
Bayan hakan ne kuma dangantakar Amurka da Isra'ilan ta yi tsami, bisa cimma yarjejeniyar da ta biyo bayan tattaunawar kasashe shida da batun nukiliyar Iran din ta shafa, ciki hadda Amurkan a watan Yulin da ya shude. (Zainab)