A wannan rana, yayin da Madam Rice ke yin jawabi a jami'ar George Washington dangane da alakar da ke tsakanin Amurka da Sin. Ta ce, a ganawar da za a yi nan ba da dadewa ba, shugaban Obama zai yi shawarwari da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping ba tare da rufa-rufa ba.
Madam Rice ta ce, a cikin shekaru 2 da suka gabata, shugabannin kasashen biyu sun yi mu'amala cikin dogon lokaci ta hanyar shawarwari na hukunce, da ba na hukunce ba, ta wayoyin tarho, ko kuma ta sakwanni, domin muddin idan kasashen biyu sun hada gwiwa, to za a warware babban kalubalen da ake fuskanta a kasashen duniya.
Rice ta ce, Amurka ta ki amincewa da ra'ayin da ke nuna cewa, ba za a kawar da rikicin da ke tsakanin Amurka da Sin ba.
Tare da jaddada cewa, kafa kyakkyawar hulda cikin armashi da zaman lafiya da kasar Sin, zai zama babbar manufar da Amurka za ta bi ta fuskar diplomasiyya cikin shekaru da dama masu zuwa.(Bako)