in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Amurka tana shirin tura sojojin musamman zuwa Iraki da Syria
2015-12-02 10:40:24 cri
Sakataren harkokin tsaron kasar Amurka Ashton Carter ya bayyana cewa, rundunar sojan Amurka tana shirin tura sojojin musamman zuwa kasar Iraki don yaki da kungiyar IS. Kuma rundunar ta shirya tsaf tana jiran umarni ne kawai ta tashi zuwa kasar Syria don kai farmaki ba zato ba tsammani.

Carter ya bayyana wa kwamitin kula da aikin soja na majalisar wakilan Amurka a wannan rana cewa, bayan da aka cimma daidaito tare da gwamnatin kasar Iraki ne, sojojin kasar ta Amurka suka kafa rukunin sojojin na musamman, kuma ayyukansu sun hada da kai hari ba zato ba tsammani, kwato mutanen da aka yi garkuwa da su, leken asiri, kama shugabannin kungiyar IS.

Carter ya kara da cewa, sojojin na musamman za su kai harin ba zato ba tsammani bisa amincewar gwamnatin kasar Iraki, kuma manufar kai harin ita ce kara tabbatar da tsaron iyakar Iraki da kara karfin jami'an tsaron kasar Iraki. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China