Shugaba Barack ya fadi haka ne a zauren Pentagone bayan ya gana da manyan masu bada shawara a fannin tsaron kasa, inda ya furta cewa, kamar yadda ya ce a baya baya, mambobin kungiyar IS sun boye har cikin yankunan birane, suna bacewa cikin fararen hula, suna amfani da maza, mata da yara da ba su iya kare kansu wajen yin garkuwa da su.
Obama ya amince da cewa, ya kamata a cimma nasarori cikin sauri. A yayin jawabinsa na biyu ga 'yan kasar Amurka ta gidan talabijin kan yaki da ta'addanci a cikin kwanaki takwas, shugaban Amurka bai bayyana wani sauyi ba kan dabarun yanzu na gwamnatin Amurka kan yaki da kungiyar IS a kasashen Iraki da Syria a lokacin da ake tsammanin zai yi sanarwa kan batun tura wani karin adadin da ba ya da yawa na sojojin Amurka zuwa kasar Iraki. (Maman Ada)