Ya ce, kafin a sanar da takunkumin da za a yi sanya mata, ya kamata Amurka ta kammala wasu ayyuka ta fuskar diflomasiyya da fasahohi, wannan ne dalilin da ya sa kasar ta jinkirta lokacin kaba wa kasar Iran takunkumi.
Game da kalubalen da kasar Amurka take kawo wa kasarsa, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ba da umurni gaggauta sarrafa makamai masu linzami na iri daban daban, haka kuma, ministan harkokin wajen kasar Ali Larijani ya ce, kasar Iran za ta ciyar da aikin yin nazari kan makamai masu linzami nan gaba a kasar.
Haka kuma, wasu na ganin cewa, matakin da kasar Amurka ta dauka na cewar sanya wa Iran takunkumi zai iya haddasa karin tabarbarewar dangantaka a tsakanin kasashen biyu, da kuma kawo illa wajen aiwatar da yarjejeniyar nukiliya ta kasar Iran yadda ya kamata. (Maryam)