in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira ga kasar Amurka da ta soke kangiyar da aka yiwa kasar Cuba a dukkan fannoni
2015-10-28 11:23:21 cri
Zaunannen wakilin Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a ranar talata 27 ga wata cewa, kasar Sin tana fatan kasar Amurka zata soke kangiyar da aka yiwa kasar Cuba a fannin tattalin arziki, kuma bangarorin biyu su bi ka'idojin tsarin mulkin MDD da na dangantakar dake tsakanin kasa da kasa don raya dangantakarsu.

An zartas da kudurin a gun babban taron MDD a wannan rana, inda aka kara kalubalantar kasar Amurka da ta soke kangiyar da ta yiwa kasar Cuba a fannonin tattalin arziki da cinikayya da hada-hadar kudi. Wannan ne karo na 24 a jere da babban taron MDD ya zartas da kuduri kamar haka.

Liu Jieyi ya yi jawabi kafin jefa kuri'u cewa, Amurka ba ta dakatar da kangiyar da ta yiwa kasar Cuba a fannonin tattalin arziki da kasuwanci da hada-hadar kudi ba, wannan ya sabawa ka'idojin tsarin mulkin MDD da kudurorin da babban taron MDD ya zartas, kuma ya kawo hasarori ga kasar Cuba a fannin tattalin arziki, da kawo cikas ga jama'ar kasar Cuba wajen kawar da talauci, da yunkurinsu na sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma cimma burin bunkasuwa na shekarar 2000, kana ya taka ikon yin rayuwa da samun bunkasuwa na jama'ar kasar Cuba, da kuma kawo illa ga yin mu'amala a tsakanin Cuba da sauran kassahen duniya a fannonin tattalin arziki da kasuwanci da hada-hadar kudi.

Hakazalika kuma, Liu Jieyi ya ce, Sin tana girmama ikon kasa da kasa na zabar tsarinsu da hanyoyin samun bunkasuwarsu, da kuma yin watsi da saka takunkumi ga wata kasa ta hanyar aikin soja ko siyasa ko tattalin arziki da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China