in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jiragen saman yakin Amurka ya tarwatsa jiragen saman jefa boma-boman Rasha
2015-10-30 11:23:50 cri
Fadar shugaban kasar Amurka ta White House ta tabbatar da cewa, jiragen saman yakin Amurka sun tarwatsa wasu jiragen saman jefa boma-bomai na Rasha a tekun Japan, bayan da wadannan jirage na Rasha suka kusanci babban jirgin ruwa mai saukar jiragen sama na Ronald Reagan.

A gun taron manema labaru, kakakin fadar White House Josh Earnest, ya ce a wannan lokaci, jirgin ruwa mai saukar jiragen sama na Amurka Ronald Reagan, na gudanar da atisayen soji tare da sojojin ruwa na Koriya ta Kudu, sai dai duk da aukuwar lamarin, hakan bai kawo fito-na-fito tsakanin sojojin kasashen biyu ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China