Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sudan ta bayyana cewa, sakamakon barkewar cutar zazzabin Dangue a karshen wata Agustar da ya shude a yankin Darfur na kasar, an samu kimanin mutane 571 wadanda cutar ta kama, inda cikinsu 133 sun rasa rayukansu.
Hukumar ta kuma ce bisa kididdiga, kimanin kashi 91.5 bisa dari cikin wadannan mutane su 571 da suka kamu da cutar, suna zaune ne a yankin Darfur, kuma adadinsu ya kai mutum 523, daga cikinsu 128 sun rasa rayukansu. Ban da wannan kuma, a cikin larduna 5 na kasar, jihar yammacin Darfur, da arewacin Darfur, na kan gaba wajen yawan masu kamuwa da cutar, inda yawansu ya kai kimani kashi 80 cikin dari.
Ya zuwa yanzu, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta tura masananta masu aikin jiyya zuwa wadannan wurare, domin jagorantar aikin dakile yaduwar wannan cuta da kuma aikin rigakafi, kana za su gudanar da hadin gwiwa da masu aikin jiyya na kasar Sudan don bada taimako yadda ya kamata. (Amina)