in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu nasarar dakile cutar kyanda a jihar Darfur ta Arewa
2015-06-07 13:55:39 cri

Kungiyar likitoci masu aikin jin kai ta kasa da kasa ko "Doctors Without Borders" a Turance, ta ce cikin watan Maris da ya gabata, ta gudanar da hadin gwiwa da ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Sudan, wajen gudanar da allurar rigakafin kamuwa da cutar kyanda a jihar Darfur ta Arewa, matakin da ya bada damar dakile barkewar cutar a jihar.

Wakilan kungiyar sun bayyana hakan ne jiya Asabar a birnin Khartoum, fadar mulkin kasar ta Sudan, suna masu cewa ma'aikatan kiwon lafiyar kasar, da jami'an kungiyar sun yiwa kananan yara wadanda ke tsakanin watanni 6 zuwa shekaru 15 su kusan dubu 270 allurar rigakafin cutar, adadin da ya karu matuka kan wadanda ake yiwa allurar a baya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China