Mataimakin wakilin musamman na MINUAD, Joseph Mutaboba da mai kula da harkokin jin kai na MDD a Sudan, Ali Al-Za Tari, sun gabatar a ranar Alhamis 27 ga wta cikin wata sanarwar hadin gwiwa inda a cikinta suka bayyana damuwarsu gaban karuwar tashe tashen hankali a Darfour.
A watan baya, yankin Darfour ya fada cikin bala'in tashin hankali da ya shafi miliyoyin jama'a. Tun farkon shekarar 2014, fiye da mutane dubu 215 suka guje wa gidajensu. Yawancin mutanen Darfour ba su da wata mafita illa tsirar da rayuwarsu dalilin jin tsoro, in ji wannan sanarwa.
Haka kuma sanarwar ta yi kira ga gwamnatin Sudan, bangarorin da abin ya shafa a cikin wannan rikici da kuma gamayyar kasa da kasa da su dauki nagartattun matakai domin kare fararen hula tare da baiwa ma'aikatun ba da agaji gudanar da aikinsu yadda ya kamata a Darfour. (Maman Ada)