Shirin samar da abinci na duniya(WFP) ya bayyana cewa, fadan da ya barke yau kusan shekaru goma a yankin na Darfur, ya raba mutane da dama daga gidajensu a yankin cikin 'yan shekarun nan, kana yana dakushe kokarin shirin na ciyar da al'ummomin da ke cikin hadari.
A cewar wani rahoto da hukumar ta fitar, sabon fadan da ya barke tun farkon wannan shekara, ya tilastawa sama da mutane 250,000 kauracewa gidajensu, inda suka bar kayayyakinsu na rayuwa, kana fadan kabilanci ya gurgunta kokarin shirin na WFP na ciyar da al'ummomin da ke cikin hadari.(Ibrahim)