Eduardo del Buey ya ce, bayan da aka kai hari ga wannan rukuni a yankin Adila, sojojin kiyaye zaman lafiya sun tura wani rukunin soja zuwa yankin don bada taimako. Ya zuwa yanzu, babu wani karin haske dangane da wannan hari.
Eduardo del Buey ya kara da cewa, tawagar UNAMID ta riga ta samu wani rahoto game da hali mai tsanani da ake ciki a yankin Adila a ranar 10 ga wata. Bayan haka ne, a ranar 12 ga wata, tawagar ta UNAMID ta samar wa hukumar yankin Darfur jirgin sama da zai tafi zuwa yankin Adila tare da sauran abubuwan taimako don taimakawa hukumar wajen kawo karshen rikicin da ake fama da shi a yankin. (Zainab)