An ce, wasu mahara ne da ba a san ko su waye ba, suka hallaka jami'in lafiyar guda da direbansa a ranar Litinin din da ta gabata, yayin da suke tsaka da gudanar da aikin na rigakafi, wanda aka fara tun ranar 24 ga watan Nuwambar da ya shude.
Da yake karin haske kan dalilan aiwatar da rigakafin, Al-Za'tari, ta bakin kakakin MDD Martin Nesirky, ya ce, Asusun UNICEF, da hadin gwiwar hukumar lafiya ta WHO ne ke daukar nauyin wannan aiki, da nufin kare yara kanana kimanin miliyan 15 dake kasar daga kamuwa da wannan cuta ta kyanda.
Daga nan sai ya yi kira da dukkanin masu ruwa da tsaki, da su tabbatar da kare rayukan ma'aikatan da ke gudanar da wannan aiki a dukkanin sassan kasar ta Sudan, tare da tabbatar da dukkanin yaran kasar sun karbi wannan allura ta rigakafi. (Saminu)