Jagoran tawagar ta UNAMID ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a gaban mambobin kwamitin tsaron MDD a ranar Laraba. Ibn Chambas ya ce, matsalar yaduwar makamai, da shigar fararen hula ayyukan ta da kayar baya a bana sun haddasa asarar rayuka fiye da wadanda aka samu yayin gwabzawa tsakanin sojojin gwamnatin da na dakarun 'yan adawa.
Daga nan sai jami'in ya bayyana matukar bukatar dake akwai ta daukar karin matakan dakile irin dimbin asarar rayuka da ake samu, tare da kafa kyakkyawan ginshikin wanzar da zaman lafiya a yankin.
Har ila yau Chambas ya bayyana bukatar bai wa dukkanin sassan da suka nuna goyon bayansu ga shirin wanzar da zaman lafiya dukkanin taimako, da karfin gwiwar da ya dace, yana mai bayyana daukar matakan siyasa wajen warware matsalar yankin na Dafur a matsayin hanya daya tilo da ta dace a bi wajen kawo karshen zub da jini. (Saminu)