Jami'an majalisar dinkin duniyar a Sudan, sun ce mafi yawa daga cikin wadanda suka arcewa batakashin, sun garzaya ne zuwa sansanonin 'yan gudun hijira na Al-Salam da Kalma wadande ke wajen Nyala babban birnin jihar South Darfur.
Mukaddashin shugaban gudanarwa na majalisar ta dinkin duniya a Sudan, Adnan Khan, ya nuna matukar damuwa a game da rahotannin dake nuni da cewa dubannnin jama'a sun gudu daga gidajen su, a sakamakon barkewar gumuzu tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai da kuma sojojin Sudan, gami da kananan kungiyoyin dakarun soji dake yankin Um Gunya a Kudancin Darfur. (Suwaiba Sule)