Ban Ki-moon ya bayar da sanarwa ta hannun kakakinsa, inda ya yi tir da wannan hari. Sanarwar ta ce, an kai hari ga ma'aikatan kiyaye zaman lafiya da suke bada kariya ga wani tabki dake dab da birnin Korma na jihar arewacin Darfur, wanda ya haddasa mutuwar ma'aikatan kiyaye zaman lafiya 'yan kasar Habasha 3. Ban Ki-moon ya jaddada cewa, ba za a amince da kai hari kan ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD ba, wanda hakan ya saba wa dokokin duniya.
A wannan wata, an sha kai hare-hare kan ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD a yankin Darfur na kasar Sudan, kasar Mali, da kasar Afirka ta Tsakiya da sauran wurare, wadanda suka haddasa mutuwar ma'aikatan kiyaye zaman lafiya fiye da 10. (Zainab)