in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 7 sun hallaka wasu 13 sun samu raunuka sakamakon barkewar sabon fadan kabilanci a yankin Darfur na kasar Sudan
2015-08-14 11:25:03 cri
A kalla mutane 7 ne aka kashe yayin da wasu 13 kuma suka samu raunuka a sakamakon barkewar sabon tashin hankali wanda ke da nasaba da fadan kabilanci a yankin Darfur na kudancin Sudan.

Jaridar Tribune ta kasar Sudan ta rawaito cewar rikicin ya kaure ne a ranar alhamis din nan tsakanin kabilun Falata da Al-Salamat dake yankin Buran wanda ke da tazarar kilomita 90 daga Nyala babban birnin kudancin Darfur.

An rawaito mataimakin babban jami'in kwamitin shura na kabilar Al-salamat Musa Al-Bashir na cewa wasu 'yan kabilar Falata ne dauke da makamai suka afkawa 'yan kabilar Al-salamat, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 7 da jikkatar wasu 13.

Ya kara da cewar akwai yiwuwar adadin wadanda rikicin ya rutsa da su zai iya karuwa, kasancewar har yanzu rikicin na cigaba da ruruwa.

Haka zalika jaridar ta Tribune ta jiyo babban jami'in kwamitin shura na kabilar Falata, Abdalla Mohamed Arsho, na cewa sabon rikicin ya barke ne sakamakon bacin rai dangane da abubuwan da suka faru a baya.

A watan Maris, makamancin wannan tashin hankali ya barke, lamarin daya haddasa hasarar rayukan mutane 67 kuma wasu daruruwa suka jikkata daga bangarorin biyu.

Fadan kabilanci ya zama babbar barazana ga yankin Darfur na kudancin kasar Sudan, kuma mahukunta da sauran jama'a sun yi ta yunkurin shawo kan matsalar amma lamarin ya faskara, kuma batu ne da ya hana ruwa gudu wajen cigaba da zaman lafiyar al'ummar yankunan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China