Mohammed ya bayyana cewa, fadar da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da sojojin 'yan tawaye ta ragu matuka a 'yan watannin da suka gabata, kamar yadda kakakin MDD Stephane Dujjaric ya sheda ma manema labarai.
Sai dai fadar kabilanci da kuma sauran laifukan da suka shafi 'yan tada zaune tsaye da miyagun laifuka na cigaba da kawo kalubale ga al'ummar yankin na Darfur. Haka kuma in ji Mr. Mohammed, rundunar sojin da 'yan sandan zaman lafiya na kungiyar UNAMID suna kara azama ta bangaren kare lafiyar fararen hula.
Mohammed ya karfafa bukatar hadin gwiwwa da kwamitoci masu karfi a kungiyar AU da manzon musamman na babban magatakardar MDD a Sudan da Sudan ta Kudu wajen shiga tsakani, inji Dujjaric.(Fatimah Jibril)