Frahan Haq ya ce bayan samun dama a ranar lahadi don a gudanar da bincike a kan zargin cin zarafin mata da 'yan mata fiye da 200 na yi masu fyade a garin dake arewacin Darfur, kwamitin na AU da MDD dake aiki a yankin UNAMID yace tun safiyar wannan rana yayi ta zagayen kauye yana tambayar mazauna da su bada bayanin iya abinda suka sani game da labarin da kafofin yada labarai suka watsa.
Kungiyar masu binciken da suka hada da wakilan 'yan sanda, sojoji da fararen hula har ila yau sun gudanar da tambayoyin ga kwamandar sojojin kasar ta Sudan, wanda a cewar Mr. Haq babu wanda ya tabbatar da faruwan haka a wannan garin na Tabit a ranar da kafofin watsa labarai suka yi ta yadawa.(Fatimah)