Mambobin majalissar dai sun bayyana takaicin nasu ne a jiya Asabar, suna masu kira da a tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan ta'asa.
Rahotanni sun ce jami'in da ya rasa ransa yayin harin na ranar Asabar dan asalin kasar Rwanda ne, ya na kuma tare da sauran wadanda suka samu raunuka, cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta UNAMID, wadda ke aikin sulhunta wasu kabilun yankin Arewacin Darfur a garin Kabkabiya, lokacin da aka kai musu harin. (Saminu Alhassan)