Mista Xie ya yi bayyani cewa, an kammala taron sauyin yanayi na birnin Paris na tsawon kwanaki 13, taron da ya gudana daga ran 30 ga watan Nuwamba zuwa ran 13 ga wannan wata. Shugaban kasar Sin Xi jinping ya halarci bikin bude taro tare da ba da jawabi mai muhimmanci. Daga karshe an kai ga cimma yarjejeniyar Paris dake shafar bangarori daban-daban cikin adalci bayan kokarin da kasa da kasa suka yi, ita ma tawagar Sin ta taka rawa mai yakini a taron.
Ban da wannan kuma, Mista Xie ya kara da cewa, yarjejeniyar ta nemi dukkannin kasashe da su dauki mataki bisa halin da suke ciki, tare da la'akari da irin bambancin dake tsakaninsu gwargwadon karfinsu, ko da yake a cewarsa, akwai wasu matsala a cikin yarjejeniyar, misali batun kudi da musayar fasahohi. (Amina)