Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana bukatar cimma yarjejeniya, wadda za ta ba da damar warware matsalar sauyin yanayi da duniya ke fuskanta, a yayin taron MDD game da sauyin yanayi dake gudana a birnin Paris na kasar Faransa.
Mr. Ban ya kara da cewa, a fannin tattalin arzikin duniya, sannu a hankali ana sauya nau'in makamashi da ake amfani da shi zuwa nau'o'in da ke fidda mafi karancin hayaki. Amma duk da haka a cewar sa akwai jan aiki, a fannin gudanar da shawarwari.
An bude taron sauyin yanayin mai lakabin COP 21 ne a ranar 30 ga watan Nuwambar da ya gabata, za kuma a rufe taron a ranar 11 ga watan nan na Disamba.(Saminu)