A daren jiyan, bangarori kimanin 200 da aka dora ma nauyin daddale yarjejeniyar tsarin tinkarar sauyin yanayi ta MDD wato UNFCCC sun amince da zartas da yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta Paris. Yarjejeniyar Paris ta yi nuni da cewa, bangarori daban daban za su kara yin kokarin tinkarar barazanar sauyin yanayi a duniya, da kiyaye karuwar yawan zafin rana kasa da digirin Celcius 2 bisa na lokacin kafin aka fara bunkasa masana'antu. Kasashen duniya za su yi kokari don cimma burin daina fitar da iska mai dumama yanayi a karshen rabin karnin nan.
Bisa yarjejeniyar, bangarori daban daban za su shiga ayyukan tinkarar sauyin yanayi ta hanyar bayar da nasu gudummawa ba tilastawa ba. Kasashe masu ci gaba za su jagoranci aikin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, da kara samar da goyon baya ga kasashe masu tasowa a fannonin kudi, fasahohi da kwarewar aiki, a kokarin taimaka musu wajen sabawa da halin sauyin yanayi.
Wakilin musamman na kasar Sin mai kula da harkokin sauyin yanayi Xie Zhenhua ya yi jawabi a gun taron cewa, yarjejeniyar Paris yarjejeniya ce mai amfani da karfi da adalci a dukkan fannoni, wadda ta alamantar da burin duniya wato na kiyaye muhalli, sabawa da sauyin yanayi da kuma samun bunkasuwa mai dorewa. Mr Xie ya jaddada cewa, kasar Sin za ta dauki alhakinta da ya dace da halin da ake ciki, da ci gaba da yin kokarin cimma burin tinkarar sauyin yanayi kafin shekarar 2020, da hadin gwiwa tare da bangarori daban daban wajen sa kaimi ga aiwatar da yarjejeniyar Paris bisa ka'idojin yarjejeniyar UNFCCC, a kokarin kafa tsarin tinkarar sauyin yanayi na duniya bisa ka'idojin hadin gwiwa da samun moriyar juna.
A nasa bangaren kuma, shugaban babban taron MDD Mogens Lykketoft ya bayar da sanarwa, inda ya yi maraba da zartas da sabuwar yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta duniya a gun taron Paris a wannan rana, ya ce, wannan yarjejeniya ta fi ma'ana bisa ga batun farfadowar dan Adam, wadda ta alamantar da ma'anar hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban yayin da suke tinkarar kalubalen duniya tare, kana ta aza tubali wajen canja tsarin tattalin arziki na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da tinkarar sauyin yanayi a duniya. (Zainab)