in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin ganin an samu sakamako mai kyau a yayin taron Paris
2015-12-12 13:34:29 cri
Wakilin musamman na kasar Sin dake kula da harkokin sauyin yanayi mista Xie Zhenhua ya bayyana a jiya ranar Jumma'a cewa, ganin an kusa rufe babban taron sauyin yanayi na Paris, a yanzu haka tawagar kasar Sin na gaggauta yin mu'amala tare da bangarori daban daban, da nufin cimma wata yarjejeniya mai amfani.

Xie ya ce, a wannan rana ya yi shawarwari tare da babban sakataren MDD Ban Ki-Moon, da ministoci da wakilai na wasu kasashe. A sa'i guda kuma sauran ma'aikata na tawagarsa su ma na yin cudanya tare da bangarori daban daban.

Xie ya kara da cewa, hadaddiyar sanarwa game da sauyin yanayi da aka cimma tsakanin Sin da Faransa, da ta tsakanin Sin da Amurka sun samar da wani shiri na kawar da bambanci tsakanin bangarorin da batun ya shafa, yana kuma mai fatan za a koyi wasu abubuwan dake cikin yarjejeniyoyin biyu.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Faransa, kuma shugaban babban taron sauyin yanayi na Paris, Laurent Fabius ya bayyana cewa, zai ci gaba da yin mu'amala tare da bangarori daban daban, za kuma a gabatar da sabon shiri a ranar 12 ga wata. Ya yi imanin cewa, za a zartas da wannan sabon shiri.

Bayan haka kuma, a yayin da yake zantawa da manema labaru, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya ce, yanzu ana fuskantar wasu matsaloli a fannonin kudi, karfin aikatawa, da yadda ake nuna banbanci kan batun da dai sauransu. Yana fata bangarori daban daban za su nuna kwarewarsu, don tsaida kuduri, ta yadda za a inganta tabbatar da rage gurbata iska, da neman dauwamammen ci gaba a duk fadin duniya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China