Sakamakon da aka samu, zai kunshi yarjejeniya game da batun taron sauyin yanayin na Paris, da kudurorin da aka cimma a yayin taron.
Fibius ya ce, an samu wannan sakamakon ne bisa daftarin da bangarorin da abun ya shafa suka mika a makon da ya gabata, da shawarwari da aka cimma a kwanaki 2 da suka gabata. Bayan da aka yi shawarwarin, bangarori da dama sun gabatar da ra'ayi guda game da inganta kwarewa game da kiyaye muhalli, kuma an warware matsalolin da aka samu na rarrabuwar kawuna da yawansu ya kai kashi 3 cikin 4. Amma kafin a cimma matsaya kan yarjejeniyar da ake saran daddalewa, akwai sauran rina a kaba.
Fabius ya ce, manyan jami'an gwamnatocin kasashen duniya za su tattauna batun kudade da ake son amfani da su game da sauyin yanayi, da matakan da za a dauka, har ma da wasu batutuwa cikin yarjejeniyar, kasancewar dukkannin kasashen duniya suna da alhakin yin aiki tare ba tare da nuna bambanci ba.
Fabius ya ce, za a samu sabon sakamakon game da shawarwarin a yammacin ranar 10 ga wannan wata. (Bako)