Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Faransa su hada kai da sauran kasashen duniya wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a taron sauyin yanayi na duniya da ya gudana a birnin Paris na kasar Faransa.
A wata zantawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Faransa Francois Hollande, shugaba Xi ya ce, yarjejeniyar ta birnin Paris ta bude wani sabon babin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa game da yadda za a tunkari matsalar sauyin yanayi nan da shekara 2020.
Shugaba Xi ya yaba da yadda kasar Faransa ta dauki bakuncin taron sauyin yanayin karo na 21. Yana mai cewa, ita ma kasar Sin ta ba da nata gudummawar don ganin an cimma nasarar ganawar.
Ya kara da cewa, nasarar da aka samu a taron na Paris ya nuna cewa, kasashen duniya za su iya magance manyan matsalolin da duniya take fuskanta ta hanyar hadin gwiwa da tattaunawa.
Da ya juya ga batun hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Faransa kuwa, shugaba Xi ya ce, a wannan shekara kasashen biyu sun samu gagarumin ci gaba a hadin gwiwar da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare
A nasa jawabin, shugaba Hollande na Faransa ya yaba da irin gudumawar da kasar ta Sin ta bayar yayin da ake daf da cimma yarjejeniyar taron.
Shugaba Hollande ya ce, yarjejeniyar da aka cimma a taron na Paris na da karfi da kuma buruka, kana ba ta saba muradun ko wace kasa ba. (Ibrahim)