Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana yau Jumma'a 11 ga wata cewa, Sin ta gamsu sosai kan sabon daftarin tsarin da aka fitar a taron sauyin yanayi na Paris. A matsayin wata kasa mai tasowa, in ji Madam Hua, Sin na fatan ganin taron zai fitar da wani tsari mai amfani da karfi da ya shafi bangarori daban-daban, kuma ita tana iyakacin kokarinta don baiwa taron gudunmawarta yadda ya kamata.
Ban da wannan kuma, a bayanin da ta yi a gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Madam Hua ta ce, Sin za ta ci gaba da goyon bayan taron, don a fitar da wani tsari mai kyau, ta yadda za a samar da wata manufa mai adalci da amfani dake iya tinkarar sauyin yanayi a duniya. (Amina)