Za'a gabatar da sakamakon karshe na matsayar da aka cimma game da dumaman yanayi na duniya a ranar Asabar din nan 12 ga wata da safe, in ji Laurent Fabius, ministan harkokin wajen kasar Faransa kuma shugaban taron akan dumaman yanayi na duniya wato COP21, domin a samu daidaita tsakanin bangarori 196 da suka sa hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi na MDD.
Kamar yadda kakakin ministan ya sanar ma manema labarai a ranar Jumma'an nan, sakamakon karshen zai kamala ne da sanyin safiyar Asabar domin a samu amincewa da shi da tsakar rana.(Fatimah)