Mr. Ban ya bayyana hakan ne ga mahalarta taron sauyin yanayi na birnin Faris. Ya ce, sanarwar hadin gwiwar Sin da Amurka game da sauyin yanayin, wadda ta kunshi manufofin kasashen biyu na shawo kan matsalar nan da shekaru 15 masu zuwa, wani babban ginshiki ne na cimma nasarar da ake fata.
Kaza lika ita ma sanarwar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Faransa game da sauyin yanayin, wadda aka sanyawa hannu yayin ziyarar da shugaban kasar Faransa ya kai kasar ta Sin a farkon watan Nuwamba, a cewar Mr. Ban, mataki ne da ya cancanci matukar yabo.
Babban magatakardar MDDr ya kara da cewa, bayan warware manyan sassan da ake da sabani a kan su game da matsalar sauyin yanayi, abu na gaba shi ne koyi daga irin yarjejeniyoyin da Sin ta kulla tsakanin ta da Faransa da kuma Amurka, bisa matsayi da kowa zai aminta da shi.(Saminu)