Hong Lei ya bayyana cewa, Sin tana sa kaimi ga cimma nasara a shawarwarin Paris. Har ma sau da yawa ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar da sanarwoyin hadin kai tare da sauran shugabannin kasashen duniya game da wannan batu, baya ga yadda ya halarci bikin bude taron na Paris, tare da gabatar da wani muhimmin jawabi kan yadda za a inganta hadin gwiwa domin tinkarar sauyin yanayi, wanda ya kasance wata muhimmiyar shawara a siyasance game da batun. Tawagar kasar Sin ta shiga shawarwarin cikin yakini bisa ra'ayin daukar nauyin dake bisa wuyanta da hadin gwiwa, wadda ta samar da gagarumar gudummawa wajen cimma yarjejeniyar Paris. Hakan ya sheda cewa, Sin ta dauki alhakinta a matsayinta ta wata kasa mai girma dake nuna kwazonta wajen tinkarar sauyin yanayi.
Hong Lei ya kara da cewa, taron Paris wani sabon mafari ne na hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa wajen tinkarar sauyin yanayi. Kasar Sin za ta yi kokari tare da kasa da kasa wajen ci gaba da samar da gudummawa kan tinkarar sauyin yanayi a duniya. (Zainab)