in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kebe kudin Sin RMB miliyan 410 wajen yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa don tinkarar batun sauyin yanayi
2015-12-07 14:04:01 cri
An shirya taron-kara-wa-juna-sani karo na 2 game da batun sauyin yanayi a yankin da aka kebe domin kasar Sin yayin taron sauyin yanayi dake gudana a birnin Paris.

A yayin taron na jiya Lahadi, wakilin musamman na kasar Sin game da batun sauyin yanayi Xie Zhenhua, ya ce a koda yaushe Sin na dukufa kamun da na'in, wajen ba da gudummawa game da tinkarar batun sauyin yanayi a duniya ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Mr. Xie ya ce daga shekarar 2011 zuwa yanzu, ban da gudummawar ta, kasar Sin ta kuma kebe kudaden da yawansu ya kai kudin Sin RMB miliyan 410 wajen tinkarar batun sauyin yanayi, da taimakawa kasashen Afrika da kasashe marasa ci gaba, da tsibiran kasashe wajen warware matsalolin sauyin yanayi a duniya.

Xie Zhenhua ya ce, har kullum Sin na sa himma da kwazo wajen inganta hadin gwiwa da kasashe masu tasowa, kaza lika a yayin da Sin ta nace kan samun ci gaban kanta, tana kuma ba da taimako ga kasashe masu ci gaba wajen warware wannan matsala. Bayan da Sin ta yi kokari har na tsawon shekaru 5, Sin ta kara mu'amala da hadin gwiwa da kasashe masu tasowa wajen tinkarar batun sauyin yanayi, kuma kasar Sin da kasashen Afrika sun karfafa niyyarsu ta yin kokari tare don kiyaye muhalli a duk duniya.

A nasu bangare mataimakin direktan hukumar kula da shirin kiyaye muhalli na M.D.D. Ibrahim Thiaw, da babban jami'in asusun kula da kiyaye muhalli na duniya Naoko Ishii, da sakataren kula da kiyaye muhalli na Swiss Bruno Oberle, da ministan kula da kiyaye muhalli da kimiyya da fasaha na kasar Nepal Krishna Chandra Paudel, da sauran manyan jami'ai jinjinawa gudummawar da Sin ke bayarwa suka yi a wannan fanni, suna masu fatan hadin gwiwa da ke tsakanin kasashe masu tasowa zai aza harsashi, na tinkarar batun sauyin yanayi, da cimma burin samun bunkasuwa cikin dogon lokaci a duniya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China