Mista Fabius ya furta cewa, abubuwa da dama sun nuna cewa, Sin tana tsayawa tsayin daka kan tinkarar sauyin yanayi. A yayin shawarwarin sauyin yanayain na Paris, Sin ta gudanar da aiki cikin yakini, kuma ta ba da shawarwari da dama, wadanda aka shigar da su cikin shawarwarin. Ya yi imani cewa, Sin za ta ci gaba da ba da gudummawa a shawarwarin, tare da ba da taimako wajen cimma nasarar babban taron Paris.
A jiya ne aka shiga matakin karshe na shawarwarin da ake kan sauyin yanayi a birnin Paris a zagaye na farko. Wakilan kasashen duniya za su yi shawarwari na karshe kan yarjejeniyar da ake fatan cimma karshen taron, a yau ne kuma ake sa ran cewa, za a tabbatar da daftari na karshe ga ministoci.(Fatima)