Mista Hong ya fadi haka ne yayin wani taron manema labaru da aka yi a wannan rana, game da wannan yarjejeniya da aka sa hannu a ran 17 ga wata a kasar Morocco mai jigon "Yarjejeniya ta fuskar siyasa ta Libya", Ya ce, abin ya kasance muhimmin ci gaban da Libya ta samu dangane da shawarwarin siyasa a kasar don haka Sin na fatan bangarorin daban-daban na kasar su ci gaba da sulhuntawa tsakaninsu don kawar da bambancin ra'ayi, ta yadda za a tabbatar da shimfidar zaman lafiya a duk fannoni tun da wuri, da farfado da kwanciyar hankalin kasar. Sin kuma na fatan hadin gwiwa da bangarorin dake da nasaba da wannan batu da su ci gaba da ba da gudunmawarsu kan tabbatar da zaman lafiya da karko a Libya har ma wannan yanki baki daya. (Amina)