Manzon Musamman mai wakiltar Magatakardar MDD a kasar Libya, Martin Kobler a ranar Larabar nan ya tabbatar da cewa, a yau Alhamis ne za'a rattaba hannu a kan yarjejeniyar siyasar kasar a Morocco.
Kamar yadda kakakin majalissar ta yi bayani ma manema labarai, rattaba hannun ya biyo bayan amincewar da dukkan bangarorin biyu dake takaddama a kan ragamar mulkin kasar wanda kwamitin tsaron MDD ta yi maraba da shi da kuma taron ministoci da aka yi a birnin Roma na kasar Italiya a ranar Lahadin nan.
Mr. Kobler ya ce, rattaba hannun an tsai da ranar Alhamis 17 ga wata ne za a aiwatar da shi, inda dimbin 'yan kasar Libyan da manyan kososhin kasashen waje da suka hada ministocin harkokin wajen kasashen waje suka tabbatar da halartarsu.
A bayanin da kakakin majalissar ya yi ma manema labarai ya ce, MDD tana cigaba da ba da goyon baya ga dukkan kokarin da kasar ta Libya za ta yi wajen ganin an kawo karshen rarrabuwan kai da ake fuskanta ta hanyar tattaunawa.
Manyan kasashen Duniya a ranar Lahadi suka kammala zagayen tattaunawarsu a birnin Roma da nufin kawo karshen takaddamar siyasar dake wanzuwa a kasar ta Libya, inda suka yi alkawarin goyon bayan MDD a shirinta na shiga tsakani da take yi.
Taron ministocin da aka kira da nufin ingiza kokarin bangarorin biyu na kasar Libyan ya amince da ranar 16 ga watan Disamba a matsayin ranar wa'adin karshe na cimma matsaya, domin samar da bukatar samun gwamnatin rikon kwarya cikin aminci da za'a mika mulki a hannun gwamnatin sulhuntawa.(Fatimah Jibril)