Manjo Janar Khalifah Haftar kuma babban kwamandan sojojin Libya ya ba da umarnin a gudanar da wani babban aikin soji a birnin Benghazi, ta hanyar amfani da babbar bindigar harba bom da sojojin sama da na kasa. Jami'in kula da harkokin yada labaru na sojojin Libya Khalifa Al-Obaidi ya gaya wa wakilinmu cewa, sojojin sun fatattaki mayakan zuwa yankin Al-Sabri, inda sojojin kasa suka kutsa cikin otel a Al-Sabri don kashe dakarun 7 na kungiyar IS gami da cafke wasu 9, ciki har da wasu 'yan kasashen waje 3.
A makon da ya gabata, Manjo Janar khalifa haftar ya kaddamar wani shirin atisaye mai taken "Lahira", inda ya ce, wannan ya zama matakin soji na karshe da za a yi amfani da shi don tabbatar da kwarjinin kasar, tun fara daukar matakan soji kan kungiyar IS a watan Mayu na shekarar bara.
Sojojin kasar Libya da ke karkashin Manjo Janar khalifahaftar wanda ya yi ritaya, sun shafe sama da shekara guda don murkushe kungiyar fafutukar kafa daular Musulunci ta IS a birnin Benghazi, mahaifar tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi da aka hambarar daga mukaminsa.(Bako)