in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar IS ta hallaka Sojojin Libya 8
2015-09-09 10:44:35 cri
A kalla sojojin Libya 8 ne suka gamu da ajalinsu sannan wasu 6 suka samu raunuka sakamakon wani harin da kungiyar IS ta kai a ranar litinin din nan a arewacin birnin Benghazi a wata cibiyar binciken ababen hawa.

Wata majiya daga gwamnatin Libya ta tabbatar da cewar mayakan na IS sun kai harin ne a litinin din nan a kan mashigar sojoji ta Nowagia dake da tazarar kilomita 8 wacce ke gabashin Benghazi a yunkurinsu na kutsawa yankin.

Tuni dai gwamnatin rikon kwarya ta Libya na gudanar da makoki ga sojojin 8 da suka mutu sannan ta jinjina musu bisa namijin kokarin da suka yi wajen sadaukar da rayuwarsu domin kare martabar kasarsu, kuma gwamnatin ta yi wa iyalan wadanda suka rasu ta'aziyya.

Da ma dai a ranar talatar nan kungiyar ta IS ta sanar a shafukanta na facebook da twitter cewar, kungiyar za ta kaddamar da hare hare a yankin na Nowagia, to sai dai sojojin na Libya sun samu nasarar hallaka dukkannin dakarun na IS kuma sannan sun lalata wasu tankokin yaki 2 da motocin daukar sojoji 2 na kungiyar.

Major Janar Khalifa Haftar mai ritaya shi ne ke jagorantar rundanar sojan Libyan wadanda ke fafatawa da mayakan na IS sama da shekara guda a birnin Benghazi, inda a nan ne rikicin kasar Libya ya samo asali tun bayan kifar da gwamnatin marigayi shugaba Muammar Gaddafi a shekarar 2011 kuma tun daga wancan lokaci ne zaman lafiya ya ta'azzara a kasar.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China