Manzon MDD yana da tabbacin tattaunawar sulhu a Libya yana matakin karshe.
Manzon musamman na Magatakardar MDD a kasar Libya, Bernardino Leon a ranar laraba ya ce tattaunawar siyasa da ake yi a kasar yana kaiwa ga shiga matakin karshe.
Ya ce watannin 7 tun lokacin da ofishin ba da goyon baya na MDD a Libya ya kaddamar da tattaunawar siyasa a Libya, yana kara samun karfin imanin cewa shirin yana matsawa ga shiga matakin karshe.
Mr Leon wanda yayi jawabi a gaban kwamitin tsaron majalissar ta hoton bidiyo daga birnin Paris, ya ce wannan aiki ya kasance mai wahala kuma cike da kalubale amma kuma ya kasance wani wanda ya iya tunkarar duk abin da ke gaban shi duk da zagon kasa da ake yi daga kowa ne bangare domin son zuciya da hana ruwa gudu wanda ke da zummar lalata shirin wanzar da zaman lafiya a Libya.
Galibin masu ruwa da tsaki na duba yiwuwar daukar wasu matakai a kokarin ganin a samu nasara da goyon baya daga tushe, alamun da ke nuna cewa, taron samar da zaman lafiyar yana samun nasara daga sassa daban-daban na al'ummar kasar Libya. (Fatimah)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku