Ta bakin mai Magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya ce Mista Kobler, zai maye gurbin Bernardino León dan kasar Spaniya ne, kuma za'a mika ragamar aikin ga sabon shugaban ne nan da 'yan kwanaki masu zuwa.
Kafin nada shi a wannan mukami, Kobler, ya kasance wakili na musamman tawagawar samar da zaman lafiya ta MDD a jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo wato MONUSCO a takaice.
A wani labarin kuma, babban jami'in bada agajin gaggawa na MDD Ali Al-Za'tari, ya yi Allah wadai da ci gaba da tsare ma'aikatan bada agaji na MDD a kudancin Libya, duk kuwa da irin kiraye kirayen da ake na neman a sako jami'an.
Al-Za'tari, ya ce sakamakon ci gaba da yin garkuwa da jami'an kai agajin zuwa kudancin Libya, lamarin ya jefa rayuwar alummar dake neman basu agajin gaggawa cikin mawuyacin hali.
An dai yi garkuwa da mutanen biyu ne Mohamed al-Monsef Ali al-Sha'lali da Walid Ramadan Salhub wadan da ke aiki da Shaik Tahir Azzawy wata kungiyar bada agaji wacce ke hagin gwiwa da sauran kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa, kuma an yi garkuwa da su ne tun a ranar 5 ga watan Yunin wannan shekara a yankin al-Shwayrif dake kudancin Libya, yayin da suke kan hanyar su ta zuwa yankunan kudancin Libyan domin gudanar da aikin rabon kayayyakin tallafi. (Ahmad)