Da ya ke zantawa da manema labarai, mataimakin kakakin wakilin na musamman Farhan Haq, ya ce, Mista Leon, ya tabbatar da cewar za'a ci gaba da daukar matakan kafa gwamnatin Hadaka a kasar, duk da irin yunkurin kafar ungulu da ake neman yiwa shirin.
Leon, ya ce galibin al'ummar Libya na bukatar ganin an kawo karshen rikicin kasar, don haka ya zama tilas a cigaba da tuntubar bangarorin da ba sa ga maciji da juna domin warware rikicin da ya dabaibaye kasar, duk da sanarwar da shugaban majaisar dokokin kasar ya bayar na yin fatali da bukatar MDD kan batun magance rikicin kasar.
Libiya ta fada cikin tashin hankali ne, yayin da tsagin gwamnati wanda kasashen duniya ke marawa baya ke takun saka da bangaren zababbiyar majalisar dokokin kasar. (Ahmad Fagam)